Coronavirus a Najeriya: Masu fama da cutar sun haura 20,000

A baya-bayan nan dai Najeriya na fitar da ɗaruruwan alƙaluman waɗanda suka kamu da cutar, wadda ta fara ɓullar a ƙasar ƙarshen watan Maris.
598
Coronavirus a Najeriya: Masu fama da cutar sun haura 20,000 [Credits: NurPhoto]

Mutane kusan 650 ne aka ba da rahoton sun sake kamuwa da cutar korona a ranar Laraba. Yanzu yawan masu cutar a Najeriya 22,020.

A baya-bayan nan dai Najeriya na fitar da ɗaruruwan alƙaluman waɗanda suka kamu da cutar, wadda ta fara ɓullar a ƙasar ƙarshen watan Maris.

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta nuna cikin alƙaluman da ta fitar a daren Laraba cewa har yanzu Lagos, inda cutar ta fi tsanani ce ke kan gaba a yawan mutanen da aka sake ganowa sun kamu, da 250.


Adadin masu korona a Lagos dai ya tasam ma 10,000. A jihar Oyo ta biyu mafi fama da korona a yankin kudu maso yammacin Najeriya, cutar ta sake kama mutum 100.

Yayin da bayanan ke nuna cewa annobar ta kashe mutum tara a Najeriya ranar Laraba.

Jihohin Filato da Delta kuma, an tabbatar mutum 40 ne suka kamu da cutar baya-bayan nan cikin kowaccensu. Sai mutum 28 a jihar Abia.

Haka zalika, an sake gano sabbin masu korona 27 a jihar Kaduna ranar Laraba. Sai Ogun, mai mutum 22.

A Edo, korona ta sake harbin mutum 20, yayin da aka gano mutum 18 ranar Larabar a jihar Akwa Ibom.

An kuma ba da rahoton mutum 17 sun sake kamuwa a jihar Kwara, da kuma makamancin wannan adadi a Abuja.

Sai Enugu, mai mutum 14, Neja da Adamawa, an gano ƙarin mutum 13 da suka kamu da korona a cikin kowaccensu.

Ƙarin jihohin da aka samu masu korona ranar Laraba, akwai Bayelsa mai mutum bakwai. Sai Osun da Bauchi, mutum shida-shida.

Anambra, mutum huɗu, sai Gombe uku, jihar Sokoto an sake gano masu korona biyu.

Jihohin Imo da Kano, mutum ɗai-ɗai a cewar alƙaluman hukumar NCDC.