Da Dumi-Dumi: Za'a Nada Lamido Sanusi A matsayin Wamban Kano, Bayan an Tsige Shi Daga kan Mulki.

Idan Baku manta ba Alhaji Lamido Sanusi Ado Bayero ne yayi takara da Tsohon Sarkin Kano Mai Martaba Muhammadu Sanusi II, bayan rasuwar mahaifinsa Mai Martaba Alhaji Ado Bayero.
1371
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero

Ran 28 Ga watan Mayun, 2021 ne ake sa ran za'a Nada tsohon Chiroman Kano, mai Murabus, Lamido Sanusi Ado Bayero a matsayin wamban Kano.

Masarautar Kano ta tabbatar da hakan ne a shafinta na Kalar sada zumunta na Facebook, in da suke chewa:

"Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Zai nada dan uwansa kuma tsohon Chiroman Kano Murabus Alhaji Sunusi Ado Bayero, sarautar Wamban Kano, ranar juma'a 28 ga watan Mayu 2021, da misalin karfe 10:00 Na safe a fadar martaba, Sarkin Kano. Allah Ya sanya alkhairi Amin. Allah taimaki sarki, ran sarki ya dade".

Tsohon Chiroman Kano Lamido Sanusi Ado Bayero

Idan baku mance ba a shekarar 2015 majalisar masarautar Kano karkashin jagorancin sarki Sanusi Lamido Sanusi II, ta tsige Alhaji Lamido Sanusi Ado Bayero daga matsayinshi na ciroman Kano, sakamakon rashin mubaya'a ga Sarki Sanusi II.

Idan Baku manta ba Alhaji Lamido Sanusi Ado Bayero ne yayi takara da Tsohon Sarkin Kano Mai Martaba Muhammadu Sanusi II, bayan rasuwar mahaifinsa Mai Martaba Alhaji Ado Bayero.