Hajj 2020: Sharuɗa takwas da Sudiyya ta gindaya kan hajjin bana

Mutum 10,000 ne kawai za su yi aikin hajjin bana amma mazauna Saudiyya kawai, ciki har da 'yan wasu kasashen da ke zama a can. Sai dai a baya can mazauna Saudiyya suna yin aikin hajji ne kawai duk bayan shekara biyar.
789
Bidiyon yadda ake wanke masallacin Manzon Allah SAW [Foto: BBC Hausa]

Ma'aikatar Aikin Hajji da Umara ta Saudiyya ta fitar da wasu sharudda guda takwas da suka shafi aikin hajjin 2020 a wata sanarwa a ranar Talata.

A ranar Litinin ne Saudiyya ta sanar da cewa mazauna kasar ne kadai - cikin su har da 'yan kasashe daban-daban da ke zaune a cikinta - za a bari su yi aikin Hajjin bana.

Cikin wata sanarwa da ma'aikatar aikin Hajji kasar ta fitar ta ce sun dauki mataki ne bisa la'akari da yadda cutar korona ta yadu zuwa kasahe sama da 180 a fadin duniya, da kuma adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar da wadanda ke dauke da ita da suka kai miliyan bakwai a fadin duniya.

Su waye za su yi aikin hajjin bana?

Mutum 10,000 ne kawai za su yi aikin hajjin bana amma mazauna Saudiyya kawai, ciki har da 'yan wasu kasashen da ke zama a can. Sai dai a baya can mazauna Saudiyya suna yin aikin hajji ne kawai duk bayan shekara biyar.

Ga dai sharuddan a jere kamar yadda ma'aikatar ta fitar:1- Za a yi wa alhazan gwajin cutar korona kafin su fara aiki, sannan za a killace su bayan an kammala aikin.2- Mazauna kasar da 'yan kasar 'yan kasa da shekara 65 ne kawai za su gudanar da aikin hajjin bana. 3- Ba za a bar utanen da ke fama da munanan cututtuka kamar su ciwon suga da ciwon zuciya su yi aikin hajjin ba. 4- Za a dinga sa ido kan yanayin lafiyar kowane mahajjaci.5- Za a dinga gudanar da ayyukan matakan aikin hajji rukunu-rukuni na mutane kadan-dkadan saboda tabbatar da dokar yin nesa-nesa da juna. 6- Yawan wadanda za su yi aikin hajjin bana ba za su haura 10,000 ba.

7- Babu wanda zai je Saudiyya don yin aikin hajji daga wasu kasashen. 8- Za a bude asibiti na musamman a Makkah don ayyukan gaggawa.

Miliyoyin mutane ke zuwa aikin hajji duk shekara daga kasashe daban-daban [Hoto: Getty Images]

Fiye da mutum miliyan biyu da dubu 500 ne suka gudanar da aikin hajjin 2019 daga fadin duniya.


SOURCE: BBC Hausa