
Mahukuntan Najeriyar sun harzuka kan abinda ya faru a wani sashi na
ofishin jakadancin Najeriyar da ke birnin Accra kasar Ghana biyo bayan
da ‘yan bindiga suka afkawa sashin ofishin suka tare da rusa shi.
Ministan kula da harkokin kasashen wajen Najeriyar Geoffrey Onyeama yace
dole ne an hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika. Kakakin
ma'aikatar harkokin wajen Najeriya
"Ya ce Najeriya ta aika da samaci ga da kiran jakadan kasar Ghana a Najeriya domin bayyana bacin ran Najeriya kan lamarin, sai dai har yanzu ba su samu wani sako daga mahukuntan Ghana kan batun ba".
Masu sharhi da nazari kan harkokin
huldar kasashen biyu na bayyana cewa hakan ya sabawa kudurin
diplomasiyya na 22 da aka rattaba hannu kansa a Vienna a kan duk wani
gini na ofishin jakadancin wata kasa da ke a wata kasar, to amma sai dai
ana ganin cewa da alamun akwai wata rashin jituwa ta fanin
dimplomasiyya tsakanin Najeriya da Ghana, duba da yadda a baya bayan nan
ake samun sabani kan batutuwa da suka shafi dimplomasiya kamar zargin
korar ‘yan Najeriya har zuwa ga rushe wani sashi na ofishin jakadancin
Najeriya a Ghana, ko da yake gwamnatin Najeriya ta
karyata.
Tuni majalisar dokokin Najeriya ta bayyana cewa tura ta fara
kaiwa bango kan al’amari na diplomasiya tsakanin kasashen biyu.
SOURCE: DW